A jiya Juma’a ne jam’iyar Thai Raksa Chart ta sanar cewa gimbiya Ubolratana mai shekaru 67 a duniya ce ‘yar takararta ta firai minister a zaben kasar na ranar 24 ga wata Maris.
Makomar siyasar gimbiyar ta huskanci matsala ne a lokacin da kaninta sarkin ya fitar da wata takaitacciyar sanarwa yana mai cewa, takarar da ‘yar uwarsa zata yi bai dace ba kuma ya sabawa gargajiya da al’adun kasar.
Jami’iyar ta Thai Raksa Chart ta fitar da wata sanarwa a yau Asabar tana fadin cewa ta amince da umarnin masarautar.
Puangthong Pawakapan malamin kimiyar siyasa ne a jami’ar Chulalongkorn, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa rashin amincewar sarkin ga takarar ‘yar uwarsa ya bata batun shigarta takara.
Jami’iyar Thai Raksa Chart ta fada a yau Asabar cewa tana mutunta gargajiya da al’adun masarautar.
Facebook Forum