Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Halaka Mutum Daya a Gidan Trump


Lokacin da wani sashin benen Trump yake ci da wuta a birnin New York. Ranar 7 Afrilu, 2018
Lokacin da wani sashin benen Trump yake ci da wuta a birnin New York. Ranar 7 Afrilu, 2018

Wata gobara da ta tashi a dogon benen gidan shugaba Donald Trumpda da ke New York ta halaka mutum guda ta kuma jikkata wasu ma'aikatan kashe gobara hudu.

Hukumomi a Birnin New York na Amurka, sun tabbatar da mutuwar mutum guda, kana wasu ma’aikatan kashe gobara hudu sun ji rauni, bayan da gobara ta tashi a katafaren benen gidan shugaba Trump da ake kira Trump Tower.

Gobarar ta tashi ne a wani daki da ke bene na 50 a gidan mai jerin benaye 58.

Rahotanni sun ce a lokacin da gobarar ta tashi da misalin karfe 5:30 na yamma agogon Amurka a jiya Asabar, babu ko daya daga cikin iyalan shugaba Trump a cikin benen.

Benen ya kasance gida ga Trump ga iyalansa a birnin na New York, kuma shi ne hedkwatarsa.

“Ba mu san musabbabin tashin gobarar ba, ma’aikatanmu sun haura zuwa sashin, mun ga yadda hayaki ya lullube sauran sashin ginin.” Inji shugaban ma'aikatar kashe gobara ta New York, Daniel Nigro.

Ya zuwa yanzu, ba a tantance mutumin da ya rasa ransa a wannan gobara ba, wacce sai da aka yi amfani da ‘yan kwana-kwana kimanin 200 kafin a shawo kanta.

Rahotanni sun ce rayuwar mutane hudun da suka ji rauni ba ta cikin hadari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG