Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Muhawara A Amurka Kan Ko A Ayyana Boko Haram A Matsayin Kungiyar Ta'adda


Hotunan wani wurin da kungiyar Boko Haram ke harhada boma bomai a Mariri Quarters dake karamar hukumar Kumbotso, jihar Kano

A yayinda Boko Haram take kai hari kusan a duk wayewar gari a arewacin Najeriya,a Washington ana tafka muhawara ko kan Amurka ta ayyana tsagerun amatsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Ahalin yanzu dai ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ayyana kungiyoyi 49 a matsayin na ta’addanci a kasashen ketare. Guda daya ce kadai daga kudu da Hamadan sahara, watau al-shabab dake Somaliya. Peter Lewis, shine darektan sashen Afirka a jami’ar John Hopkins dake nan Washington.

Yace babu kokonto Boko-Haram mummunar kungiyar gwagwarmaya ce, duk da haka yace zai kasance kuskure ga ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta saka ta cikin jerin kungiyoyi data ta ayyana a matsayin na ta’adda.

Bamu da isassun bayanai illa gaskiyar da aka sani cewa Boko Haram ta rikide ta zama mummunar kungiyar mayakan sakai, ba wai kawai matsalar tsaro ko kalubale ba, amma sanin cewa wan nan kungiya tana da tsari kuma mai karfi a a gwagwarmayar da take yi a arewacin Najeriya.

Lewis yace babu cikakken bayani gameda shugabancin kungiyar da watakil alakarta da wasu kungiyoyi daga ketare.Yace babban abinda aka sani shine yankin yana fama da talauci, cin-hanci da rashawa, gwamnati maras kyau,da kuma dambarwar addini,cikin wan nan yanayi ne Boko Haram take harkokinta.

Mutum daya da yake goyon bayan a saka Boko Haram cikin jerin kungiyoyin ta’adanci shine tsohon jakadan Amurka a najeriya Howard Jeter. Bai goyi bayan Lewis ba a wani taro da aka yi a baya bayan a Washington.

“A hakikan wan nan kungiyar ta’addanci ne.Amma Peter yace kada a ayyanata haka ba.Ina son inji bayaninka da zai hana a saka ta cikin jerin kungiyoyin ta’adanci ba. Kungiyar ta’’addanci ne. Idan ka kashe mutane 28 da basu aikata laifin kome ba da suka hadu a coci, wan nan kungiyar ta’addanci ne.

Jeter yana maganan harin bam ranar kirsimeti a bara a wani kauyen Abuja, babban birnin Najeriya. A wasu hare haren Boko Haram ta auna jami’an tsaro da musulmi.

Ahalinda ake ciki kuma, jami’an tsaro sun tsananta matakan tsaro a wata fitacciyar kasuwa dake birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar, bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko-Haram ne suka kai kan kasuwar ranar litinin.

Rundunar sojojin Najeriya tace ta kashe mayakan sakai takwas a musayar harbe harbe da suka yi, kodashike Boko Haram tace ba a kashe ko daya daga cikin membobinta ba.

Wani kakakin kungiyar ta Boko Haram wadda ya kira kansa Abu Qaqa, ya gayawa manema labarai ta woya cewa sun kai harin ne domin ramuwar gayya kan ‘yan tireda a kasuwar da suka mika wani dan kungiyar ga hukumomi cikin makon jiya.

Wasu majiyoyi daga sassan kiwon lafiya da kuma wasu ‘yan kasuwa sunce an kashe akalla farar hula 30 wadanda musayar harbe harben suka rutsa dasu, kodashike rundunar sojojin najeriya ta musanta an kashe farar hula.

Wani babban malami a fannin halayya da zamantakaewa jami’ar Abuja, Abubakar Umar kari, yace zuwa yanzu dai Boko Haram ta sami biyan bukatar tursasawa abokan adawarta.

“Babban tasirin haka shine talakawa a Maiduguri da kuma wasu wurare daga yanzu zasuji kara jin tsoron kai karar take taken kungiyar gun ‘yansanda domin kungiyar zata iya auna harin ramuwar gayya akansu. Kuma babu abinda jami’an tsaro zasu iya na azo a gani wajen kare su.duk da cewa ‘yan tsegumi kan kungiyar da ma sauran ‘yan Najeriya wadanda suke da kishin kasar sun kosa da take taken Boko Haram.

Ya kara da cewa wan nan lamari zai kara tsananta rashin yarda da tuni ake fama dashi tsakanin mazauna yankunan da kuma jami’an tsaro.

“ Ban sani ba ko yana daga cikin yadda aka horas dasu ko kuma ba sa bin ka’idojinda aka shimfida dangane yadda zasu tinkari abokan fada ba. Jami’an tsaron Najeriya kawai sai su kama harbin kan mai uwa da wabi a duk lokacinda suka fuskanci jayayya da kungiyoyi dake dauke da makamai.

Wani mai bincike na kungiyar kare hakkin Bil-Adama ta Human Rights watch, Eric Gutchuss, yana nazarin wuce gona da iri da ake zargin jami’an tsaro suke yi amatsayin martani da suke dauka kan hare haren Boko Haram, ciki har da kai farmaki kan jama’a da kona gidajen mutane da ake zargin suna baiwa ‘yan Boko Haram mafaka.

“Mazauna yankunan suna cikin tsaka mai wuya, domin suna fuskantar barazana daga duka sassan biyu.Daya daga Boko Haram dayan kuma daga jami’an tsaro. Wan nan ne ginshiki, jami’an tsaron Najeriya tilas su mutunta hakkin Bil-Adama kan irin wadan nan hare haren, domin idan ba haka ba, abinda wadan nan kungiyoyi suke amfani dashi kenan, suna amfani da cin zarafin mutane cikin al’uma a matsayin hanyar janyo hankalin mutane su shiga kungiyar domin su sami hujjar jaddada hare hare da suke kaiwa. Domin jami’an tsaro su sami nasarar aikinsu suna bukatar goyon bayan jama’a.

Kungiyar Boko Haram a duk wuni tana kai hare hare kan cibiyoyin soja da ‘yansanda da kuma musulmi da kirista a a rewacin Najeriya. Gwamnatin tarayya tana fama da kokarin shawo kan barazanar da kungiyar take yiwa tsaron kasa.

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG