Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amurka Na Dari-dari Da Tayin Tattaunawa Da Koriya ta Arewa Ta Yi


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Gwamnatin shugaba Trump a nan Amurka na dari-dari da tayin da Koriya ta Arewa ta yi na tattaunawa sai idan tayin na nufin kasar Koriyan ta yi watsi da shirinta na mallakar makaman nukiliya ne

Gwamnatin shugaba Trump tana nuna dari-dari da aniyar da Koriya ta Arewa ta bayyana ta yin tattaunawa da Amurka.

Kakakin fadar shugaban Amurka ta White House, Sarah Huckabee Sanders, ta ce "Zamu sanya ido mu ga ko sakon da Pyongyang ta bayyana yau, na sha'awar tattaunawa da Amurka, na nufin matakin farko ne na yin watsi da makaman nukiliya a bangarenta. A yanzu kuwa, tilas ne Amurka da sauran kasashen duniya su ci gaba da bayyanawa Koriya ta Arewa a fili cewa, shirinta na nukiliya da na makamai masu linzamai ba za a taba amincewa da su ba."

Ta bayyana cewa Amurka da Koriya ta Kudu, da ma sauran kasashen duniya, sun yarda cewa tilas ne duk wata tattaunawar da za a yi da Koriya ta Arewa ta kai ga raba kasar da duk wani makamin nukiliya. Tilas a ci gaba da gagarumin matsin lambar da ake yi har sai Koriya ta Arewa ta rabu da makaman nukiliya. Kakakin ta ci gaba da cewa, kamar yadda shugaba Trump ke cewa akwai falala mai tarin yawa ga Koriya ta Arewa muddin ta watsar da batun mallakar makamin nukiliya’.

Sanders dai tayi wannan maganar ce a lokacin da take kasar ta Koriya ta kudu sa'ilin da ta raka diyar shugaba Trump, Ivanka, jiya lahadi wajen bikin rufe gasar wasannin motsa jiki na hunturu na Olympics a Pyeongchang.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG