Accessibility links

Gwamnatin Jihar Filato Zata Yiwa Harkokin Sufuri Garambawul


Gwamnan Jihar Filato

A jihar Filato gwamnatin ta fara shirin yiwa harkokin sufuri garambawul musamman harkokin babura masu kafa uku da aka sani da keke napep

A wani yunkuri na daidaita harkokin sufuri a jihar Filato musamman yadda ake anfani da babura masu kafa uku ko keke napep gwamnatin Filato zata yiwa shirin sufuri garambawul.

Gyaran da gwamnati ke son yi ya zama wajibi ne domin yawan baburan ya fi abunda gwamnatin ta kayyade tun can farko. Kwamishanan Sufuri Alhaji Abubakar Dashe yace a tsarin da gwamnatin ta tsayar da kuma majalisar dokoki ta amince da shi yawan kekunan ba zai wuce dubu hudu ba a cikin birnin Jos. Amma yau an wayi gari sai gashi yawansu ya kai dubu talatin.

A shirin gwamnati duk kekunan yakamata a yi masu ragista kamar yadda ake yiwa motoci. Kamar yadda aka gano akwai kekuna da yawa da basu da rajista. Sabili da haka gyaran da gwamnati zata yi ta tanadi kama duk baburan da basu da ragista. Kwamishanan yace da zarar an kafa dokar za'a soma kama kekunan kuma ba za'a sakesu ba sai sun yi ragista. Yace idan an shiga wasu sassa a cikin garin Jos za'a ga kamar babu doka da oda. Gyaran ya zama dole domin a dauki matakan tsaro. Yace abun mamaki akwai wata tasha cikin anguwar Nasarawa Gwam inda ake zirga-zirga daga nan tashar zuwa Jamhuriyar Niger. Ya kamata a ce hukuma ta san da tashar. Idan aka bar irin wannan tashar za'a samu damuwa kan tsaro. Yace akwai tashoshi barkatai wadanda tuntuni aka basu wasiku su kwashe nasu-i-nasu.

Shugaban kungiyar masu tuka keke napep reshen jihar Filato Yakubu Jatau ya bayyana cewa kodayake sun amince da duk wani gyara da gwamnati zata kawo amma akwai abun dubawa. Ya roki gwamnati ta gyara hanyoyin da suke bi domin a rage masu damuwa. Wani mai tuka keke napep Shatimu Dashe Shimankar yace talauci ne ya sa kekunan suka yi yawa. Mutanen Igbo dake kasuwanci da yawancinsu yanzu sun bari suna tuka keke napep domin ko ta halin kaka mutum zai samu abun yin cefane kowace rana.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG