Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 700 Don Yaki Da Ta’addanci


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate).

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya mika bukatar karin kasafin kudaden da za a yi amfani da su wajen kawar da barazanar tsaro da ta addabi sassa daban-daban na kasar.

Shugaba Mohammadu Buhari ya aikawa Majalisar Dokokin Najeriya wani dan kwarya-kwaryan kasafin kudi wanda a ciki ake kyautata zaton za a samu kudaden inganta tsaron kasa domin sayen kayan yaki da dakile ayyukan 'yan ta'adda.

Sai dai kwararru a fannin tsaro na cewa an dade ana zuba kudade amma kwaliya ba ta biyan kudin sabulu, inda wasu ‘yan kasa kuma na ganin akwai wadanda ke hana ruwa gudu a gwamnatin.

Wannan kasafi dai shi ne kuma har wa yau za a yi amfani da shi wajen samo rigakafin cutar Coronvirus da kuma na cuta mai karya garkuwar jiki HIV ko SIDA.

Shugaban kwamitin kula da sha'anin sojojin kasa a majalisar dattawa Mohammed Ali Ndume, ya ce wannan shi ne karo na farko da ake mika irin wannan bukatar ga Majalisar kuma wannan zai taimaka wajen kawo karshen rashin kayan aiki da jam'ian tsaro suke nema wajen magance matsalar tsaro da aka kwashi shekaru 12 ana fama da shi a kasa.

Sanata Mohammed Ali Ndume - Shugaban Komitin Kula da Harkokin Sojojin Kasa a Majalisar Dattawa
Sanata Mohammed Ali Ndume - Shugaban Komitin Kula da Harkokin Sojojin Kasa a Majalisar Dattawa

Majalisar za ta yi gaggawan amincewa da kasafin, kuma za ta yi aiki tare da bangaren zartarwa wajen ganin an samu nasara a yaki da 'yan ta'adda in ji shi.

Amma kuma kwararre a kimiyar tsaro ta kasa da kasa Dokta Yahuza Ahmed Getso, ya ce Allah ya sa wannan karon hakar ta cimma ruwa, domin a baya an cire zunzurutun kudade har Naira triliyan 2 ko fiye da haka, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Dokta Getso ya kara da cewa wannan karon ma idan ba a yi hankali ba, ba za ta chanja zani ba.

Sai dai ga wani masanin harkokin siyasa Sa'idu Yaro Tafawa daga karamar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, ya ce a yi wa wasu gargadi, musamman ministan kudi ta kasa akan muhimmacin wadannan kudade, saboda kasar tana cikin wani hali.

Sa'idu Tafawa ya sake cewa idan aka fitar da kudaden cikin sauri, akwai alamun za a samu saukin matsalar tsaron idan an sayi makamai da jami'an tsaron ke bukata kuma akan lokaci.

An ware sama da Naira biliyan 700 daga cikin Naira biliyan 895 na karin kasafin kudin don magance duk wasu matsalolin na rashin tsaro da ke addabar kasar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

Gwamnatin Najeriya Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 700 Don Yaki Da Ta’addanci
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00


Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG