Accessibility links

Yan Bindiga Sun Kashe Sama Da Dalibai 40 A Yobe

  • Grace Alheri Abdu

Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ya ziyarci wadansu da aka kaiwa hari

Wadansu mahara sun kashe a kalla dalibai 40 a wani hari da suka kai da asuba a wata kwaleji dake jihar Yobe

Wadansu mahara da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe a kalla dalibai 40 a wani hari da suka kai da asuba a wata kwaleji dake arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar soja Eli Lazarus ya shaidawa Muryar Amurka cewa, ‘yan bindigan sun kai hari ne a makarantar ayyukan noma ta jihar Yobe yau lahadi da asuba suka bude wuta kan daliban da ke kwance suna barci.

Ana jinyar a kallar dalibai 18 da suka ji raunuka a wani asibiti dake Damaturu babban birnin jihar. Makarantar tana kan hanyar Gujiba dake kimanin tazarar kilomita 50 da babban birnin jihar.

Jihar Yobe tayi fama da kazaman hare hare da ake kyautata zaton kungiyar Boko Haram ke kaiwa a cikin watannin nan. A cikin watan Yuli, mayaka sun kai hari a wadansu dakunan kwanan ‘yan makaranta a jihar suka kashe dalibai 29 da malami daya.

Ana kuma dorawa kungiyar alhakin kashe daruruwan mutane a cikin shekarar nan kadai, a hare haren da suka rika kaiwa gine ginen gwamnati da kasuwanni da makarantu da kafofin sadarwa da kuma majami’u.

XS
SM
MD
LG