Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Yi Taron Farfado da Yankin


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Biyo bayan umurnin Shugaba Muhammad Buhari gwamnonin jihohin arewa maso gabas sun yi taron samo bakin zaren warware matsalolin da suka addabi yankinsu

Gwamnonin sun duba sabbin matakan dawo da tsaro da farfado da tattalin arzikin yankin.

Cikin jihohin shida uku sun fi fuskantar ta'adancin Boko Haram yayinda sauran ukun ke samun nasu kason jefi- jefi da kuma zama tamkar tundun mun tsira ga sauran 'yan jihohin.

Gwamna Abubakar Muhammad shi ya dauki bakuncin taron gwamnonin. Yace sun karbi rahoto na musamman daga kwamitin da gwamnonin yankin suka kafa tun shekarar 2013.

Kwamitin ya shirya babban taron koli na farfado da tattalin arzikin yankin. A wannan lokacin gwamnan jihar Gombe shi ya jagoranci shirin. Tun daga lokacin ba'a samu daman karbar rahoton ba. Dalili ke nan suka hallara a gidan gwamnatin Bauchi dake Asokoro Abuja aka karbi rahoton.

Rahoton ya kunshi hanyoyi na farfado da tattalin arzikin shiyar arewa maso gabas. Ya kuma kunshi shirin yadda za'a sake gina wuraren da ta'adancin Boko Haram ya daidaita.

Yanzu dai kawar da shingayen sojoji bai yawalta a arewa maso gabas ba saboda halin tsaro da yankin ke ciki.

Wasu 'yan sa kai da suka hada da 'yan banga da mafarautan barayi na ganin lokaci yayi da za'a basu dama su bada tasu gudummawa wajen samarda tsaro musamman ma da lamarin ya hada da 'yan fashi da makami da barayin shanu da masu sace mutane don samun kudin fansa.

Shehu Aljan dake aiki da 'yansanda na wajen yaki da barayi nada wannan irin ra'ayin. Yace irinsu 'yan kunar bakin wake a jeji ya kamata a kirawo a zauna dasu su horas da 'yansanda a jeji. Idan zasu yi wata daya dasu a jeji zasu zakulo barayin shanu da masu satar mutane da 'yan fashi da makami su shigo dasu domin a ragesu. Yace ba yawan yawo cikin gari ba da 'yansanda ke yi suna muzgunawa mutane ba. Yace a basu wata uku zasu kawar dasu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG