Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Habasha Ta Amince Ta Sakarwa Eritrea Yankinta


Shugaban Eritrea yace zai tura tawaga zuwa Habasha domin tattaunawa a kan alkawarin da shugaba Firai Ministan Abiy Ahmed ya dauka na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a shekarar 2000

Amincewa da aiwatar da yarjejeniyar, yana nufin Habasha ta amince ta sakarwa Eritrea yankinta kana kuma zata mutunta hukuncin kotun kasa da kasa na shekarar 2002 da ya baiwa Eritrea ikon yankin Badme da kasashen biyu ke takaddama akai.

Shugaban Eritrea Isaias Afwerki ya sanar da wannan sabon labari ne a Asmara, a jawabinsa na shekara-shekara da akea tunawa da wadanda suka yi mutuwar shahada. Yace tawagar zata tattauna a kan ci gaba da aiwatar da shirin tsakanin kasashen biyu.

Daga bisani, shugaban ma’aikatar fadar firai ministan Habasha Fitsum Arega ya aike da sakon Twitter yana cewar, Firai ministan yana marhabi da tawagar Eritrea.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG