Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi A Afirka Ta Kudu Sun Samu Nasarar Shawo Kan Gobarar Da Ta Kona Ginin Majalisar Dokokin Kasar


Gobara ta Kama Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:48 0:00

Gobara ta kama majalisar dokokin Afirka ta Kudu.

Hukumomi a Afirka ta Kudu sun ce an samu nasarar shawo kan wutar da ake zaton wani mutun ne ya kunnata wacce ta kone ginin majalisar dokokin kasar, bayan gobarar ta shafe kwanaki biyu ta na tafka barna.

Mummunar gobarar a ginin majalisar dokokin ta ta shi ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta kone ofisoshi tare da haddasa ruftawar rufin ginin majalisar dokokin. Yayin da jami’an kashe gobara ke kokarin shawo kan gobarar, wani bakin hayaki da wuta sun yi ta tashi sama a birnin Cape Town da ke kudancin kasar.

Kimanin jami’an kashe gobara 70 ne suka yi aikin sama da sa’o’i bakwai bayan tashin gobarar da sanyin safiya, in ji jami’ar hukumar kashe gobara ta Cape Town Jermaine Carelse. Wata na’ura mai daga mutane sama ce ta daga wasu daga cikinsu domin fesa ruwan kashe gobarar.

Ba a samu rahoton jikkata ba, kuma dama an rufe majalisar domin hutu.

Da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, shugaban kasar, Cyril Ramaphosa, ya ce ana tsare da wani mutum kuma ‘yan sanda suna yi masa tambayoyi dangane da gobarar.

Wani mutum mai shekaru 49 da ake zargi da tayar da gobarar ya bayyana a gaban kotu domin fuskantar tuhume-tuhume biyar da suka hada da kona ginin, da kuma mallakar wani abu mai fashewa. Lauyan wanda ake tuhumar Zandile Christmas Mafe ya ce ya musanta zargin kuma ba zai amsa laifinsa ba.

-AP/Reuters

XS
SM
MD
LG