Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyar ‘Yan Rwanda Da Aka Kora Daga Nijar Ta Shigar Da Kara A Kotu


Firai Ministan Nijar, Ouhmoudou Mahamadou (Twitter/ Ouhmoudou Mahamadou)

Lauyar dake kare ‘yan Rwandar nan da gwamnatin Nijar ta kora daga kasar ta bayyana damuwa a game da abinda ta kira rashin mutunta alkawuran da kasar ta dauka a yarjejeniyar da suka cimma da MDD akan batun bai wa wadanan mutane mafaka.

Saboda haka ne lauyar ta aike wa hukumomi wasika domin su janye wannan kudiri da ya sabawa doka yayinda a wani bangare ta fara yunkurin garzayawa kotu.

A taron manema labaran da lauyar ta kira a wannan juma’a 31 ga watan Disamba, lauyar dake kare ‘yan Rwandan su takwas da gwamnatin Nijar ta bukaci su fice daga kasar kafin ranar 3 ga watan Janairu 2022, Me Kadidjatou Hamadou ta fara da tunatar da su akan hanyoyin da aka bi wajen bai wa wadanan mutane mafaka.

Wannan ya sa lauyar rubutawa Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou wasika don sanar da shi irin illolin dake tattare ga matakin da gwamnatin ta dauka, wanda tuni ta fara yunkurin kalubalantarsa a kotu.

Wadanan ‘yan Rwanda takwas da suka sami mafaka a Nijar a karshen watan Nuwamba da ya gabata, na daga cikin wadanda kotun ta hukunta su akan masu hannu a kisan kiyashin 1994, ta gurfanar inda ta wanke wasu daga cikinsu wadanda aka kama da laifi kuwa sun kammala zaman wakafin da aka yanke masu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Lauyar ‘Yan Rwanda Da Aka Kora Daga Nijar Ta Shigar Da Kara A Kotu
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00


XS
SM
MD
LG