Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Ceto 180 Saura 30 Daga Cikin Daliban Kaduna Da Aka Sace


Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa'i

Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbar da sace daliban kolejin horar da shi'anin gandun daji dake yankin Mando a Karamar Hukumar Igabin jahar Kaduna, sai dai ta ce an ceto dalibai dari da tamanin (180).

'Yan Mata Daga Cikin Daliban
'Yan Mata Daga Cikin Daliban

'Yan-bindigar da su ka fasa katangar kwalejin dai sun shiga wurin kwanan daliban ne da karfe 11:30 na dare amma jim kadan bayan fitar su sai jami'an tsaro su ka tare su, inda bayan musayar wuta aka ceto dalibai dari da tamanin (180) yayin da har yanzu talatin (30) ba a san ina suke ba, inji kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan.

'yan Maza Daga Cikin Daliban
'yan Maza Daga Cikin Daliban

Daya daga cikin Daliban wannan makaranta ya ce harin ya girgiza su, musamman ganin lokacin da kuma inda abin ya auku. Har zuwa yammachin Juma'ar nan dai iyaye da 'yan'uwan daliban na cikin damuwa gameda wannan matsala. Kamar yadda wasu daga cikin iyayen daliban su ka bayyana.

Wannan hari dai na zuwa ne kwana daya da karbar rahoton tsaro da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, inda gwamna Nasiru Ahmed El-rufai ya jadda cewa ba sulhu tsakanin gwamnati da 'yan-bindiga.

Rescued Abducted Kaduna school Children.
Rescued Abducted Kaduna school Children.

Dalibai 42 cikin wadanda aka ceto dai mata ne, 130 kuma maza sai kuma ma'aikatan makarantar guda takwas (8).

Ga cikakken rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00


XS
SM
MD
LG