Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Nijar


Wani harin kunar bakin wake da aka kai a Maiduguri
Wani harin kunar bakin wake da aka kai a Maiduguri

Rahotanni daga garin Diffa na cewa a wajejn karfe goma na daren jiya litinin wasu 'yan kunar bakin wake suka kutsa wata makarantar allo dake unguwar Diffa Kura inda suka tayar da bama bamai.

Sakamakon wucin gadi ya ce lamarin ya haddasa mutuwar mutane tara cikinsu har da 'yan kunar bakin waken uku, yayin da mutane 35 suka ji rauni. Wata majiyar kiwon lafiya da ta bukaci a saya sunanta tace a ciki akwai mata biyu da namiji guda da suka tada bam din .

Yanzu haka almajirai da malaman da wannan harin ya rusta da su na can kwance a asibitin Diffa domin ci gaba da jiyya.

Shugaban majalisar mashawartan yankin diffa ya tabbatar da faruwar wannan al'amari, ko da yake ya ce har yanzu suna cikin harhada bayanai.

Yankin Diffa na daga cikin yankunan da gwamnatin Nijar ta kafawa dokar ta baci domin murkushe hare haren boko haram. kuma rahotanni na cewa harin kunar bakin waken na jiya, ya sa hukumomi suka dauki tsaurara matakan tsaro a dukka wajejen taron jama'a, musamman a ciki da wajen kasuwar garin Dfiffa wacce take ci a kowacce Talata.

Saurari Rahoton Souley Moumouni Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG