Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kula Da Fansho na Najeriya Ta Tattauna da Tsoffin Sojoji


Nigerian soldiers on patrol. (File photo)

Da yake jawabi ga tsoffin sojojin Najeriya, shugabanFansho na mayakan Najeriya, Air Vice Marsharl Mohammed Dikko yace rundunar sojan kasar na daukar sabbin matakai da naura mai aiki da kwakwalwa wajen tantance masu karban fansho a gidan soja.

Sai dai da aka tambayi AirVice masharl Dikko ko wasu abubuwa ne za a gani sabbi da ya sha ban-ban dana baya, ga amsar da ya bayar.

‘’ka ga yanzu idan aka tantance su da kumfuta da daukar hoton yatsun su, kamar yadda aka tantance masu jefa kuria a zaben da ya gabata sai kana da katin din-din-din zaka jefa kuria, to kaga ta haka za a gane wadanda suka sa sunayen bogi’’

‘’Na biyu kuma wannan zaisa mu samu ingantaccen bayanai da muke bukata zamu tabbatar abinda muka adana game da bayanai mun gamsu dashi, a baya z aka ga cewa akwai wasu tsoffin sojoji da suka mutu ba a sanar damu sai kaga fansho dinsu yana ta zuwa a ajiyar na banki ba tare da munsani ba, sai idan yan uwansu sunzo sunce muna wadannan fa sun rasu sai mu tambaya muce wani wata ne, to kaga duk irin wadannan zai kau’’

Ga Hassan Maina Kaina da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

XS
SM
MD
LG