Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam Ta Kama Motoci Dubu Uku A Najeriya


Hukumar kwastan a Najeriya ta kama motoci kimanin dubu uku tun daga farkon wannan shekara zuwa yanzu. bayan makamai data sha kamawa a can baya.

Tuni dai hukumar Kwastam ta hana shigowa da motoci ta kan iyaka sai ta tashohin ruwan Najeriya, a wata sanarwa da hukumar da fitar wanda kakakinta Joseph Atta, ya rattabawa hannu, wadda ke cewa matakin da hukumar ta dauka na kumshe ne a karkashin dokar hukumar, sashe na 147.

Sai dai kuma masu sayar da motoci a Nageriya, sun fara kokawa dangane da samamen da hukumar ta kwastan ke kaiwa a ofisoshi da shagunan su ko kuma wuraren da suke sayar da motoci, inda suka zargi hukumar da musguna masu.

Alhaji Mohammed Ali, shine babban kwantirola mai kula da shiyyar Seme-Boda, dake kan iyakar Najeriya, da Benin, kuma ya bayyana cewa dalilin kama mota shine domin tantance takardun rajistar mota, dan haka suna bin Kadin tsarin hukumar ne.

Ko a farkon watannan da muke ciki hukumar ta kama wasu motoci goma sha daya na alfarma da aka kyasta kudin su ya kai Naira miliyan dari da ashirin da biyar da lugo hudu, da suka hada da motoci kirar Lexus Jeep, da Toyoya, da Marsandi da manyan motocin daukar kaya.

Mohamed Uba, shine kwantirolan hukumar dake kula da shiyya ta daya ya bayyana cewa dalilin daya sa suka kara kaimi shine domin shigowa da makamai da ake yi a kasar.

Domin karin bayani saurari rahoton Babangida Jibrin daga Legas.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:24 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG