Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya Ta Duniya Zata Tura Allurai Dubu 900 Na Rigakafin Kwalara


Hukumar kiwon lafiya ta duniya zata tura allurai dubu 900 na rigakafin cutar kwalara zuwa Bangladesh domin shawo kan annobar cutar da ta barke a wani sansanin ‘yan gudun hijirar Roghingya dake shake da mutane a bakin iyakar Bangladesh da Myanmar.

Kimanin ‘yan kabilar ta Rohingya, wadanda Musulmi ne, rabin miliyan sun tsallaka bakin iyakar domin tserewa daga farmakin da sojoji ke kaiwa kan kauyukansu.

A kasar Yemen ma, wata mummunar annobar ta cutar kwalara ta shafi mutane rabin miliyan, inda Hukumar kiwon lafiya ta Duniya take kyautata zaton cewa yawan wadanda suka kamu da cutar zai karu zuwa miliyan daya nan da karshen shekara.

Mutane kimanin dubu 100 suke mutuwa kowace shekara a fadin duniya a sanadin cutar kwalara.

A ranar talata, Hukumar kiwon lafiya ta duniya da gwamnatocin kasashe, da kungiyoyin agaji sun bayarda sanarwar shirin kawar da cutar kwalara daga doron duniya nan da shekarar 2030. Wannan shine karon farko da aka fito da irin wannan shiri na kawar da kwalara.

Sai dai kuma, Dr. Amesh Adalja ya ce ba zai yiwu a iya kawar da cutar kwalara kwata kwata daga doron duniya ba a saboda kwayar halittar cutar dake janyowa tana nan baje a ko ina. Adalja kwararre ne kan cututtuka masu yaduwa a Cibiyar Kare Lafiyar Bil Adama ta Jami’ar Johsn Hopkins.

Ya shaidawa Muryar Amurka cewa zai yiwu a rage bullar cutar a kasashen Bangladesh da Yemen kamar yadda aka dakile ta a Amurka. Yace tsabta, it ace muhimmiya ga dakile cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG