Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe Ta INEC Tana Ci Gaba Da Tattara Sakamakon Zabe


Shugaban INEC Da Daraktocin Hukumar Zaben Kasa

Hukumomin zabe a Najeriya suna can suna ci gaba da tattara bayanan kuri’un da aka jefa a babban zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayyar da aka gudanar a kasar jiya Asabar.

Zaben na jiya ya fuskanci hatsaniya da tashe-tashen hankula a wasu sassa na jihohin arewa-maso-gabas da ma wasu wurare a kudancin kasar.

Jim kadan kafin a soma jefa kuri’un ne aka ji karar harbe-harbe suna tashi a wasu sassa na garin Maidugurin jihar Borno dake can arewa-maso-gabascin Nigeria kuma, bayan da suka musanta labarin harin da farko, daga baya hukumomin tsaron na Nigeria sun fito sun amsa cewa lalle wasu mayakan Boko Haram ne suka yi yunkurin kutsowa zuwa cikin garin na Maiduguri, inda suka rinka harbe-harbe.

Amma dai duk da wannan kalubalan da aka samu, dukkan alamu na nuna cewa an samu nasarar shiryawa da kuma gudanar da zaben ba tare da wasu manyan matsaloli ba.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG