Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi A Nijar Sun Kama Shugaban Kungiyar Hadin Kan Al’ummar Jihar Tilabery


Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)
Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)

Hukumomin jamhuriyar Nijar sun kama shugaban kungiyar hadin kan al’umar jihar Tilabery Amadou Harouna Maiga bayan da ya yi wasu kalamai dangane da zanga-zangar nan ta matasan da suka datsewa ayarin motocin sojan Faransa hanya a garin Tera a ranar 27 ga watan November 2021.

Tun a yammacin Talatar da ta gabata ne ‘yan sandan farin kaya suka cafke shugaban kwamitin hadin kan al’umar ta jihar Tilabery Amadou Harouna Maiga sannan suka gabatar da shi a gaban kotun birnin Yamai a washe gari inda lauyan gwamnati ya saurare shi kafin a fice da shi zuwa gidan yari.

Tsohon sakataren kungiyar kwadago ta USTN Amadou Harouna Maiga na daga cikin wadanda ke sukar lamirin gwamnatin Nijar dangane da yadda take tafiyar da harkokin tsaro a yankin Tilabery mai fama da hare haren ‘yan ta’adda. Saboda haka abokan tafiyarsa ke ganin bai dace a kama shi ba don a cewarsu gwagwarmayar samar da tsaro suka sa gaba ba wani abu ba.

Wani mutum mai suna Mounkaila Daouda yace sun je ne harabar kotu domin baiwa shugabanni goyon baya. ya ce, siyasa a cikin wannan al’amari suna kokowa ne saboda matsalar tsaro za ci gaba da wannan fafutuka muddin aka ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a Tilabery.

Sai dai bayanai na cewa tsohon Ministan tsaro Kalla Moutari ne ya shigar da kara a gaban kotu saboda abinda ya kira kazafin da shugaban kwamitin hadin kan jihar Tilabery ya yi masa bayan wata hirar da ya yi da manema labarai game da yadda yake kallon tarzomar da aka fuskanta a garin Tera a ranar 27 ga watan November da ya gabata. Amma Jami’in kare hakkin jama’a a jihar Tilabery Ibrahim Mamoudou na fatan ganin an yi sulhu a wannan al’amari.

Tsohon Ministan tsaro dan majalisar dokoki Kalla Moutari da Muryar Amurka ta tuntuba bai so ya yi magana akan wannan batu ba domin a cewarsa magana ce dake gaban shari’a.

Sha’anin tsaro a yankin Tilabery wani abu ne dake kara tsananta, inda farkon mako kamfanonin hada hadar sakwanin kudade su ka bada sanarwar rufe wasu ofisoshi a jihar mai makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari akan irin wadanan ofisoshi suka kwashi miliyoyin cfa kafin su cinna wuta.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Hukumomi A Nijar Sun Kama Shugaban Kungiyar Hadin Kan Al’ummar Jihar Tilabery
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00


XS
SM
MD
LG