Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi a Legas Sun Ce Kar Kowa Ya Je Cibiyar Rigakafin COVID Ba Tare Da Izini Ba


Shugaba Buhari Yana karbar rigakafin COVID
Shugaba Buhari Yana karbar rigakafin COVID

Gwamnatin jihar Legas a Najeriya ta ce ba za ta lamunta da mutane masu tafiya cibiyoyin allurar rigakafi ba tare da sun samu cancantar yin hakan ba saboda ta himmantu ne wurin tabbatar da ganin aikin rigakafin coronavirus ya yi nasara.

Kwamishinan kiwon lafiya a jihar Legas, Professor Akin Abayomi ya hikikance a yau Alhamis cewa ‘yan Legas da suka cancanci samun allurar rigakafin COVID-19 a zangon farko na aikin bada rigakafin da ke gudana, dole ne su rubuta sunayensu ta shafin yanar gizo da aka bude wa aikin kafin ziyartar wani daga cikin cibiyoyi 88 na alluarar rigakafin.

Abayomi ya ci gaba da fadin cewa rubuta sunayen wani tsari ne da aka tilasta yin sa a aikin bada rigakafin a jihar Legas.

Yayin sake duban tsare tsare da aka yi wa aikin bada allurar rigakafin, Abayomin ya ce mutanen da suka cancanci samun allurar rigakafin COVID-19 a zangon farko na aikin bada rigakafin da ke gudana, su ziyarci shafin da hukuma ta bude su cike takardar bayanansu da za a iya tantancewa da cibiyar da suke so su karbi allurar da ranar da suke so da kuma lokaci.

Mutanen da ke da cancantar su yi wannan rajistar tsakanin sa’o’i 24 zuwa 48 kafin ranar da suke so a musu alluarar. “Wannan wani mataki ne na tabbatar da an bi ka’idar karbar allurar mai inganci, cikin sauri, sumul ba tare da bata lokaci ba da kuma hana cunkoson jama’a a wuraren allurar rigakafin.

Muna bada kwarin gwiwa ga duk ‘yan Legas da za a musu allurar rigakafi bisa cancantar da aka tsara a zangon farko na aiki da su yi amfani da wannan shafi da hukumar ci gaba kiwon lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA) ta samar domin samun gurbin zuwa karbar allurar rigakafin, inji shi.

Ya yi bayani cewa, bayan nasarar rubuta suna kafin allurar, shafin zai bada takardar allurar da kuma sakon dake tabbatar da samun gurbi, kana za a tura sakon imel ga duk wanda ya samu cancantar samun alluar rigakafin.

Da yake maida martani a kan rahoton cewa mutanen da ba su cikin wadanda suka cancanci samun allurar a zangon farko na iya shiga cincirindo a wuraren allurar, Abayomi ya yi kashedi cewa irin wadannan mutane kar su kuskura su je wurin.

Gwamnatin Legas ba zata ci gaba da jure irin wannan hali ba, sai dai ta himmantu ne wurin tabbatar da ganin wannan aiki ya yi nasara.

XS
SM
MD
LG