Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ilhan Omar Na Fuskantar Kalubale A Zaben Fidda Gwani Na Democrat


Ilhan Omar 'yar majalisar wakilai
Ilhan Omar 'yar majalisar wakilai

Jihohi biyar na Amurka suna gudanar da zabuka a jiya Talata, da ya hada da 'yar majalisa daga jihar Minnesota Ilhan Omar, babbar mai sukar Shugaba Donald Trump, ta fuskantar kalubale mai tsauri a zaben fidda gwani na jam’iyyar Democrat a gundumar Minneapolis.

Omar, ‘yar asalin Somalia, tana daya daga cikin matan musulma ta farko da aka zaba zuwa Majalisa. Ta sake tsayawa takara a wa’adi na biyu bayan shafe shekara biyu, abokiyar karawar ta Antone Melton-Meaux, wata lauya bakar fata wacce, kamar Omar, ta tara sama da dala miliyan 4 a cikin yakin neman zabe amma ta yi gabanta a cikin 'yan makonnin nan.

Omar na daya daga cikin ‘yan majalisa ‘yan democrat hudu wadanda suke kiran kansu "The Squad". Sun sha ja-in-ja da Trump a cikin shekaru uku da rabi da yayi a Fadar White House, yayin da a wasu lokuta kuma suke kara da shugabannin jam’iyyar Demokrata kan manufofin da basa daukar ci gaba sosai.

Omar da Melton-Meaux sun bayyana kansu a matsayin masu neman ci gaba amma sun bambanta a kan matsayin su game da Isra'ila. Omar ta nuna rashin goyon baya ga kokarin kawar da kai daga kasar ta Yahudu game da yadda take yi wa Falasdinawa, yayin da Melton-Meaux ta samu goyon bayan wasu kungiyoyin Isra’ila da dama.

Har ila yau masu kada kuri'a sun jefa a kananan hukumomi, jihohi da kuma mazabu a jihohin Connecticut, Wisconsin, Vermont da Georgia.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG