Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Indonesiya Za Ta Binciki Cin Zarafin Jami'in Diflomasiyyar Najeriya


Ma’aikatar harkokin wajen Indonesia ta bayyana nadamar ta bayan da jami’an shige da fice a Jakarta suka tsare wani babban jami’in diflomasiyya na Najeriya karfi da yaji, lamarin da ya sa gwamnati ta kira jakadanta da ke Abuja don tuntuba.

Bidiyon abin da ya faru, wanda aka yada a kafafen sada zumunta kuma ya haifar da cece -ku- ce, ya nuna mutumin da ke tsaren a hannun wasu mutane da yawa cikin matukar damuwa.

"Ba na iya numfashi," in ji shi a cikin bidiyon, yana ihu yayin da aka manne kansa a wurin zama.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana mutumin a matsayin "wakilin diflomasiyyar Najeriya da aka amince da shi" a ofishin jakadancin Najeriya da ke Jakarta, ba tare da bayyana sunansa ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Indonesiya Teuku Faizasyah ya ce a ranar Alhamis ma'aikatar ta yi nadamar faruwar lamarin ranar 7 ga watan Agusta, kuma tana ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Najeriya kan lamarin.

"Wannan lamarin, keɓebben lamari ne kuma ba shi da alaƙa da alkawarin Indonesia na aiwatar da ayyukanta a matsayin ƙasa mai masaukin baki kamar yadda yarjejeniyar Vienna ta shafi dangantakar diflomasiyya," in ji shi.

Ya kara da cewa "ma'aikatar doka da kare hakkin dan adam ta kaddamar da bincike na cikin gida domin bin diddigin lamarin".

Faizasyah ya ce an tsakanin ma'aikatar da jakadan Najeriya a ranar Laraba inda suka tattauna kan "kyakkyawar alakar" tsakanin kasashen.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya kira shi "babban laifin cin mutuncin kasa da kasa daga hanun Indonesia".

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Esther Sunsuwa ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa, "Gwamnatin Najeriya ta bukaci takunkumin da ya dace kan jami'an da abin ya shafa kuma ta kira jakadanta a Indonesia don tuntuba, gami da bitar alakar kasashen biyu."

Ofishin kula da shige da fice na Indonesia ya kare matakin jami'anta, yana mai cewa jami'in diflomasiyyar ya ki bada haddin kai lokacin da ake masa tambayoyi a gaban wani gida, yayin da wani jami'i ya ce yana yin bincike na yau da kullun game da izinin zamar kasar baki a hukumance.

Ibnu Chuldun, shugaban dokar Jakarta da hukumar kare hakkin dan adam da ke kula da shige da fice, ya fadawa wani taron manema labarai cewa jami’in diflomasiyyar ya ki ya nuna katunan sa, sannan daga baya yayi kokarin fasa tagar motar da zungurun tabar sigari lokacin da aka kama shi, abun da yayi sanadiyar da raunin daya daga cikin jami'an.

XS
SM
MD
LG