Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Tana Kara Bunkasa Samar Da Makamashin Uranium Kasar


Shugaban Iran Hassan Rouhani
Shugaban Iran Hassan Rouhani

Iran ta fada ajiya Litinin cewa ta ninka karfin makamashin uranium nata sau hudu, a lokacin da cacar baki tsakanin Tehran da Washington ke ci gaba da yin zafi.

Jami’an kasar Iran sun ce ana inganta makamashin uranium dinne domin makamashi da fararen hula ke amfani da shi, wanda bai kai karfin makamashin da aka amincewa da shi ba a cikin yarjejeniyar shekara ta 2015.

Mai yiwuwa ba da dadewa ba Iran zata zarce adadadin makamashin da aka bukaci ta adana a cikin wannan yarjejeniya.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya sanar a makwanni biyu da suka gabata cewa zai fice daga wasu bangarori na yarjejeniyar nukiliya tsakanin kasashe shidda, da ta hada da yanayin da Iran zata iya sayar da wani adadin makamashin uranium ga wasu kasashe.

Rouhani ya yi barazanar Iran zata iya kaiwa matsayin kera makamai da makamashin idan bata sami sassaucin tattalin arziki da aka yi mata a yarjejeniyar kafin farkon watan Yuli ba.

Shugaban Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar shekara daya da ta gabata. Ya kuma sake kakabawa Tehran takunkumai kana ya yi barazanar kara wasu takunkuman a kan kasashe da suka ci gaba da kasuwanci da Iran. Shawarar da Trump ya yanke ta kara raunana tattalin arzikin Iran wanda dama yake fama da matsaloli.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG