Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Janye Jakadunta a New Zealand Da Senegal


Shugaban Israila Benjamin Netanyahu

Firai ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya fara daukan matakan diplomasiyya akan kasashen da suka goyi bayan kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya nemi Isra’ilan ta dakatar da gine-gine da ta ke yi a yamma da kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus.

A yau Asabar, Netanyahu ya umurci Jakadansa a New Zealand da na Senegal da su koma kasashensu domin tuntuba.

New Zealand Senegal na daga cikin kasashen da suka bukaci a kada kuri’a kan lamarin, baya ga kasashen Venezuela da Malaysia.

Amma da farko Masar ce ta fara gabatar da wannan bukata ta dakatar da gine-ginen da Isra’ilan ke yi.

Amma ta janye a ranar Alhamis, bayan wata tattaunawa ta wayar talho da shugaba Abdel Fatah al sisi da zababben shugaban Amurka Donald Trump suka yi.

Amurka dai ta dauki wata matsaya ce da ba ta taba dauka ba, yayin kada kuri’ar, wato ta hau kujerar yan ba-ruwanmu.

Wannan matsaya da aka cimma a kwamitin sulhun, sam bai yi wa Isra’ila dadi ba kamar yadda jakadan Isra’ila a majalisar Danny Danon ya nuna.

“Wannan kuduri da aka cimma a yau, zai shiga jerin matakan da ake dauka na abin-kunya a majalisar na muzgunawa kasar Isra’ila.”

Su kuwa Falasdinawa, farin ciki suka nuna da kudirin majalisar wanda zai hana Isra’ila ci gaba da gine-gine a yankunansu, Riyad Mansour, shi ne Jakada mai sa’ido na Palasdinu a Majalisar.

“Mun gamsu da cewa, a karshe kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da wannan muhimmin batu, wanda za a iya mai kallon lamari ne mai cike da tarihi, wanda zai ci gaba da kare kudirin samar da kasashe biyu.”

XS
SM
MD
LG