Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kai Hari Kan Filin Tashin Jiragen Saman Sojojin Syria


Wani yanki na Syria da aka kai hari
Wani yanki na Syria da aka kai hari

Rasha da Syria sun nuna korafinsu bayan da wasu jiragen yakin Isra'ila suka kai farmaki a sararin samaniyar kasar Lebanon.

Kasashen Syria da Rasha sun bayyana cewa jiragen yakin Isra’ila guda biyu da ke aiki a sararin samaniyar Lebanon sun kai hari wani hari filin tashin jiragen saman sojojin a tsakiyar Syria.

Amman sojojin Isra’ila ba su yi magana akan hare-haren da aka kai a sansanin T4 da ke Lardin Homs ba.

Kungiyar kare hakkin bil adama da ke da hedkwata a Birtaniya, ta ce mutane 14 sun mutu ciki har da dakarun kasar Iran.

A watan Febrairun da ya gabata ne Isra’ila ta zargi sojojin Iran da amfani da wannan sansanin wajen aika jirgin sama mara matuki zuwa kasar Israila su kuma suka maida martini ta hanyar kai hari kan sojojin saman Syria da sojojin Iran da ke cikin Syria.

Kuma Firayi Ministan Isra’ila Benjamin Nethanyahiu ya yi alkawarin maida martani ga duk wanda ya kai musu hari.

Syria dai ta ci gaba da musanta amfani da makaman guba a cikin yakin da ya faro tun daga shekarar 2011 har da na baya-bayan nan da ake zargi a harin da aka a ranar Asabar din da ta gabata.

Harin an kai shi ne a yankin da ke karkashin ikon ‘yan tawaye a wajen garin Damascuss wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 40.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG