Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Ta'adda Sun Kashe Sojojin Nijer 16 A Yankin Tillia A Cikin Jahar Tahoua


‘Yan bindiga
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:15 0:00

Lokacin jana’izar wasu da ‘yan bindiga suka kashe

Yan ta'adda da ake kyautata zaton sun bullo daga kasar Mali ne, sun yi wa askarawan Nijar da ke sintirin tsaro da wanzar da zaman lafiya a yankin Tillia dake arewacin jahar Tahoua kwatan bauna, inda suka kashe soja 16

Rahotanin da ke fitowa daga arewacin jahar Tahoua a jamhuriyar Nijer su na nuna cewa a ranar 1 ga watan mayun nan da muke ciki, an wa rundunar askarawan kasar da ke yawon sintiri a yankin Tilliya na Garde Nationale du Nijer wajajen garuruwan Ekenewane da Intazey kwantan bauna wajan karfe 5:20 na yamma.

Wadansu mutane ne a kan babura sama da 100 dauke da makamai da ba a fayyace su ba, suka abkawa rundunar inda suka hallaka soja 16, suka kuma yi awon gaba da motoci 2, suka lalata mota daya.

Sojoji 6 sun raunata kuma suna assibitin Tahoua. Su kuwa sojojin kasar, sun hallaka da yawa daga cikin maharan da kuma lalata kayan su na yaki suka tsere da su daga bisani.

Ana kyautata zaton yan tsaurin kishin addinin islama ne da ke kutsowa a wannan iyakar ta Nijer da Mali suka aikata wannan danyen aiki. A baya su na abkawa fararen hulla ne kawai, sai gashi yanzu sun wa askarawan kasar wannan kwantan bauma.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG