Jam’iyar ANC da Democratic Alliance da kuma sabon tashe jam’iya mai hankoron farfado da tattalin arziki Economic Freedom Fighters sun yi gangamin yakin neman zaben su na karshe a Johannesburg babban birnin kasuwancin kasar.
Jam’iyar ANC tana kan gaba da sauran jam’iyu 48 da suka tsaya takara, sai dai jam’iyar dake mulkin kasar tun shekarar alib da dari tara da casa’in da hudu tana fuskantar suka kan batun cin hanci da rashawa. Shugaban jam’iyar, kuma shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya amince da haka a jawabinsa ranar Asabar.
Ramaphosa yace sun amince da cewa sun tafka kurakurai, kana yace sun kuma zo gaban al’ummar su saboda sun yarda da kasawar su, yace sai dai wadanda basu yin komi ne kawai basu kuskure.
Bisa ga cewar hukumar zabe, ‘yan Afrika ta Kudu miliyan ishirin da shida da dubu dari bakwai ne suka yi rajistar kada kuri’a a zaben da za a gudanar gobe Laraba.
Facebook Forum