Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaro Sun Halaka ‘Yan Bindiga Sama Da 200 A Jihar Nejan Najeriya


Wani dan fashin daji a Najeriya

Bayanai dai sun nuna cewa a yanzu haka akwai daruruwan garuruwa da suka zama tamkar kufai a wasu yankuna na kananan hukumomin Rafi, da Shiroro, da kuma karamar hukumar Mariga.

Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta bayyana cewa gamayyar Jami’an tsaro sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga sama da 200 a jihar.

Jihar Nejan dai na fama da matsalar ‘yan bindiga da suka addabi jama’a da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa sannan da kona gidajen jama’a da kuma kisan mutane.

A wani taron manema labarai kwamishinan kananan hukumomi da masarautu da kuma tsaron cikin gida na jihar Nejan, Mr. Emanuel Umar ya ce gamayyar jami’an tsaron da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya na civil defence da kuma ‘yan banga sun tafka wani gumurzun da ya sa suka samu nasarar halaka wadannan ‘yan ta’adda a garuruwan Babban Lamba dake yankin karamar hukumar Kontagora da kuma Kundu ta karamar hukumar Rafi. Amma kuma suma biyu daga cikin jami’an tsaron sun rasa rayukkansu.

hakan na zuwa ne a daidai lokacin da al’umar jihar Nejan ke kara nuna damuwa akan halin zaman zullumi da fargabar wadannan ‘yan fashin daji.

Alhaji Awaisu Giwa Kuta wanda shugaban al’umma ne a jihar Nejan ya ce kadan ya rage ‘yan bindigar su aukawa birnin Minna fadar Gwamnatin jihar.

Bayanai dai sun nuna cewa a yanzu haka akwai daruruwan garuruwa da suka zama tamkar kufai a wasu yankuna na kananan hukumomin Rafi, da Shiroro, da kuma karamar hukumar Mariga, a sakamakon yadda wadannan ‘yan fashin daji suka tarwatsa al’ummomin dake zaune a cikinsu

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Jami’an Tsaro Sun Halaka ‘Yan Bindiga Sama Da 200 A Jihar Nejan Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG