Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Gwamnatin Trump Ya Rasa Aikinsa


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Amfani da kudin gwamnati wajen shatar kananan jiragen sama da wani jami'in gwamnatin shugaba Donald Trump ya yi, ta sa ya rasa aikinsa.

Wani jami’in gwamnatin shugaba Trump ya rasa aikinsa saboda shatar kananan jirgen sama mai tsada da ya yi wajen gudanar da ayyukansa, wadanda ake cire kudin daga aljihun gwmanati, maimakon ya rika bin jirgin saman ‘yan kasuwa mai safarar fasinja, wanda ake biyan kudi mai rahusa.

Wata sanarwa da Fadar White House ta fitar a jiya Juma’a, ta nuna cewa Thomas Price, wanda shi ne Sakataren ma’aikatar kiwon lafiya da kula da ayyuka da suka shafi al’uma, ya mika takardar ajiye aikinsa, wacce shugaba Trump ya amince da ita.

Da karfe 12 daren jiya, murabus din da Sakatare Price ya yi, ya fara aiki, inda tuni mataimakin sakataren kiwon lafiya kuma Darektan hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka, Don J. Wright ya karbi mukamin mukaddashin ma’aikatar.

Sa’a guda gabanin Price ya mika takardar ajiye aikinsa, Shugaba Trump ya fadawa manema labarai cewa bai ji dadin abinda Price ya yi ba, lura da yadda jama’a suke al’amarin.

Trump ya kara da cewa, jami’an gwamnatinsa za su iya daukan shatar jirgin sama ne kawai idan har sun amince za su biya kudin daga aljihunsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG