Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Kim Jong Un Na Ci Gaba Da Jefa Kalaman Batanci a Junansu


Shugaba Kim Jong Un (daga hagu) shugaba Donald Trump (daga dama)
Shugaba Kim Jong Un (daga hagu) shugaba Donald Trump (daga dama)

Amurka da Korea ta arewa na ci gaba da jefawa juna kalamai marasa dadi, inda a baya-bayan nan wani babban jami'in gwamnatin Korea, ya mayarwa da shugaba Donald Trump martani kan kalamansa na baya nan.

Ministan harkokin wajen Korea ta arewa ya mayarwa da shugaban Amurka martani kan kiran shugaba Kim Jong Un da ya yi a matsayin "mutum mai roka" wanda yake so ya halaka kansa.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa zauren Majalisar Dinkin Duniya, Ri Yong kwatanta Trump a matsayin "mutum mai tabin hankali da giyar mulki ke daukansa."

A lokacin da ya gabatar da jawabins a gaban Majalisar, shugaban Amurka Donald Trump ya kwatanta takwaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim Jong Un a matsayin "mutum mai roka."

A ranar Juma’ar da ta gabata, shugaba Trump ya gargadi Kim a shafinsa na Twitter, inda ya ce “Kim Jong Un na Korea ta arewa, wanda yake da tabin hankali, wanda kuma bai damu da yadda yake azabtar da mutanensa da yunwa ba, da kashe su da yake yi, zai ga jarrabawar da bai taba gani a baya ba.”

Sanarwar Shugaba Kim har ila yau, martani ne ga jawabin da shugaba Trump ya yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya a wannan makon, inda ya kira shi a matsayin “mutum mai roka” wanda ya dauki hanyar halaka kansa da kansa.

Trump ya kuma kwatanta gwamnatin Kim a matsayin ta “azzalumai” inda ya jaddada cewa, idan ta kama Amurka ta kare kanta da kawayenta, za ta shafe Korea ta arewa daga doron kasa baki daya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG