Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaridar Washington Post Ta Bin Diddigin Yawan Mutanen Da 'Yan Sanda Suka Kashe


Har yanzu babu raguwa akan yawan mutanen da 'yan Sanda ke kashewa a Amurka.

Wani shirin bin diddigin da jaridar Washington Post ke gudanarwa a nan Amurka ya nuna cewa adadin mutanen da ‘yan sanda suka harbe har lahira a watanni 6 na farkon wannan shekara, kusan daidai yake da adadin wadanda suka harbe har lahira a daidai irin wannan lokaci a cikin shekaru biyun da suka shige.

Jaridar ta ce ‘yan sanda a Amurka sun harbe suka kashe mutane 492 a watanni shida na farkon wannan shekara. Wadanda aka fi kashewa, turawa ne maza wadanda suke rike da bindigogi ko wasu makamai a lokacin. Kashi 25 cikin 100 na wadanda ake kashewa suna da tabuwar hankali. Amma kuma, kashi 25 cikin 100 na wadanda ake kashewa bakaken fata ne, duk da cewa yawansu a cikin kasa kashi 6 ne kawai cikin 100.

Jaridar Washington Post ta fara bin diddigin harbe-harben da ‘yan sanda kan yi a bayan kashe Michael Brown da suka yi a garin Ferguson dake Jihar Missouri.

Duk da zanga zanga da kiraye kirayen sauya manufofin hukumomin ‘yan sanda da aka yi tun wancan lokacin, har yanzu babu raguwar da aka gani ta yawan mutanen da ‘yan sandan ke kashewa.

Har ila yau jaridar ta ce yawan ‘yan sandan da ake kashewa a bakin aiki shi ma bai canja ba a cikin shekaru biyun da suka shige.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG