Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jayayya Tsakanin Hukumomin Tsaro Na Mummunar Illa Ga Yaki Da 'Yan Ta'adda - Dr. Audi


Dr. Ahmed Audi-shugaban hukumar taron NSCDC.
Dr. Ahmed Audi-shugaban hukumar taron NSCDC.

Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta “Civil Defense”, Dakta Ahmed Audi, ya fada cewa kishi da hassada a tsakanin hukumomin tsaron kasar na kara ta’azzara rashin tsaro a cikin kasar.

Dakta Ahmed Audi ya kuma yi kira ga kwamandojin hukumar a jihohin da su sa hannu, a yunkurinsa na yi wa rundunar gyarar fuska domin jami’ai su yi aiki ko kuma su fice.

Kwamandan na hukumar tsaron farin kaya, ya yi jawaban ne yayin da ayarin sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubair Jibril Mai Gwari II, wanda ‘yan bindiga suka kai masa hari a kan babbar hanya da yammacin ranar Talata.

Karin bayani akan: jihar Katsina​, Dr. Ahmed Audi​, Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan ta’adda ne suka kai samame a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, inda suka kashe wani mutumin da aka gano mai suna Ibrahim Kwatahi kana su ka sace kananan yara biyu.

A halin da ake ciki kuma, majalisar wakilai a jiya ta kafa wani gagarumin kwamiti da zai yi fashin baki a sha’anin tsaro a cikin kasar kana ya fito da hanyoyin shawo kan batun da majalisa za ta mika ga shugaba Muhammadu Buhari​, a cewar kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila.

Kishi da hassada tsakanin hukumomin tsaro ne ke kara cusa rashin tsaro a Najeriya inji Audi, a wani jawabi da ya yi wurin bude wani taron wuni biyu na bada horo game da tabbatar da kyawawan dabi’u wurin karfafa dokar kare ‘yancin dan Adam da aikin hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma sasanta rikici da aka shirya wa kwamandodinsa.

Ya na mai fadin cewa akwai bukatar fidda kishi da hassada tsakanin hukumomin a wannan yaki da ake yi na magance batun rashin tsaro.

XS
SM
MD
LG