Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Yaki na Najeriya Ya Bace a Adamawa

Alpha Jet Najeriya (File Photo)
Alpha Jet Najeriya (File Photo)

Rundunar sojojin Najeriya ta gaskata rahotannin dake cewa wani jirgin saman yaki na kasar da ya tashi daga Yola domin gudanar da shawagin aiki ya bace tun jiya babu labarin abinda ya same shi.

Rundunar sojojin Najeriya ta gaskata rahotannin dake cewa wani jirgin saman yaki na kasar da ya tashi daga Yola domin gudanar da shawagin aiki ya bace tun jiya babu labarin abinda ya same shi.

A cikin wata sanarwar da ya bayar yau lahadi, darektan yada labarai na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Chris Olukolade, yace wannan jirgi ya bar Yola jiya asabar da misalin karfe 10:45 na safiya, kuma an yi tsammanin zai komo sansaninsa zuwa karfe 12 na rana.

Yace wannan jirgin yaki kirara Alpha-Jet mai lamba NAF-466, yana dauke da matuka guda biyu, kuma duk kokarin da aka yi na tuntubarsa ko sanin inda yake ya ci tura.

A halin yanzu dai, rundunar sojojin ta Najeriya ta kaddamar da wani gagarumin aiki na nemo inda wannan jirgin ya shiga ko abinda ya same shi.

XS
SM
MD
LG