Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Dokokin Somalia Ya Yi Murabus


Shugaba Somalia, Hassan Sheikh Mohamud

Rahotanni daga Somalia na cewa, Kakakin Majalisar Dokokin Somalia, ya yi murabus daga mukaminsa sanadiyar wata takaddamar siyasa da ta kaure a fagen siyasar kasar.

Jami’ai sun sanar da cewa Kakakin Majalisar Dokokin Somalia, Mohammed Osman Jawari, ya sauka daga kujerarsa bayan wani sa-in-sar siyasa da aka kwashe makwannin uku ana yi da Firai ministan kasar.

Ministan tsarin mulkin kasar, Abdirahman Hosh ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce kakaki Jawari ya mika takardar ajiye aikinsa.

Dan majalisa Hussein Arab ma ya shaidawa wakilin Muryar Amurka saukar kakakin daga kujerarsa, inda ya ce “ mataimakin kakakin Abdeweli Muddey ne ya karanto mana takardar barin aikin kakakin da safiyar yau”.

Daya daga cikin mukarraban Jawari ya shaidawa Muryar Amurka cewa ya yi murabus din ne bisa zabin kansa.

Facebook Forum

Matsalar Tsaro A Zamfara

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Kamu A Auren Nupawa

Yadda Nupawa Suke Kamun Ango A Bikin Aure
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG