Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Faransa Ta Gargadi ‘Yan Kasar Da Su Guji Zuwa Kasashen Yankin Sahel Saboda Barazanar Sace Mutane


Shugaban Kasar Faransa Macron 
Shugaban Kasar Faransa Macron 

Kasar Faransa ta gargadi ‘yan kasar ta su guji yawo a cikin kasashen Yankin Sahel da daina zuwa yawon bude ido a cikin wadanan kasashen don gudun sace su ko kuma a kashe su, biyo bayan karuwar aika-aikar ‘yan ta'adda a kan ‘yan kasar Faransa.

BIRNIN N’KONNI, NIGER -Kasar ta Faransa ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da ta fitar farkon wannan watan.

A sanarwa da ta wallafa a shafin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Faransa jiya Litinin, wadda aka wallafa tun ranar 07 ga wata April na wannan shekara ta 2023, ta gargadi, mutanen kasar Faransa dake cikin kasashen Yankin Sahel da su daina yawo a cikin wadanan kasashen, kuma kar su saki jiki ko da a wuraren da suke, suna zaton akwai kwanciyar hankali.

Kasasashen da Faransa ta tsawaci mutanenta da zuwa yawon bude ido ko yawo a cikin su, sun hada da Jamhuriyar Nijer, Mali, Chadi, Burkina Faso da Mauritania da ma makwabtansu.

Faransa ta ce, wannan sanarwar na da nasaba da karin yawan “kyamar kasar Faransa da mutanen ta a Yakin Sahel, da kuma karin kai hare - hare da kungiyoyin yakin Jihadi suka kara tsaurarawa a wadanan kasashen” musaman a iyaka uku, da ta hada da kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

Yan Nijar musamman kugiyoyin fararen hulla da masanan tarihin huldar kasa da kasa sun mayar da martani akan wannan sanarwar kasancewa Nijar daya ce daga kasashen da Faransa ta gargadi mutanen ta da su bar yawo a cikin su ko kuwa yawon bude ido. Suna masu cewa, duk da yake Faransa ba su goyon bayan ayyukan ta’addanci da tasa wata kasa gaba, za su yi na’am da ficewar Faransa daga kasashen domin a cewarsu, girke dakarun a kasashen na assasa ayyukan ta’andanci.

Sanarwar ta kasar Faransa na zuwa ne kwanaki kalilan bayan sakin ‘dan jarida nan Olivier Dubois da kungiyar yakin jihadi a Yankin Sahel GSIM ta yi biyo bayan kokarin hukumomin Jamhuriyar Nijar na ceto shi.

Yawan zangar da a ke yi a kasashen Yamacin Africa na nuna kyamar Faransa ana iya cewa ya soma tasiri da ma jefa fargaba ga hukumomin kasar Faransa dangane da makomar su a kasashen na Yankin Sahel.

Saurari cikakken rahoto Harouna Mamman Bako:

Kasar Faransa Ta Gargadi ‘Yan Kasar Da Su Guji Zuwa Kasashen Yankin Sahel Saboda Barazanar Sace Mutane.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

XS
SM
MD
LG