Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Hungary Ta Dakatar da Yiwa Bakin Haure Rajista


Wasu dake nman mafaka a kasar Hungary
Wasu dake nman mafaka a kasar Hungary

Kasar Hungary ta ce za ta jingine aikin yin rijista ga masu neman mafaka a kasar, saboda karuwar adadin bakin haure da ya fara haifar da matsi ga ababan more-rayuwa.

Wani Kakakin gwamnatin Hungary ya ce kasar ta sanar da abokan huldanta na kungiyar tarayyar Turai ta EU, kan wannan mataki na jingine aikin yin rijistan na dan wani lokaci.

Akwai wani shiri tsakanin mambobin kasashen kungiyar ta EU, da ya baiwa masu neman mafaka damar yin zirga zirga a tsakanin mambobin kasashen, sai dai8 shirin ya tanadi cewa masu neman mafaka za su nemi tarkardun iznin zama ne kawai a kasashen da suk fara shiga.

Bayanai na nuni da cewa Hungary ta shiga matsalar samun masu zuwa kasar domin neman mafaka tun daga shekarar da ta gabata, baya ga kasashen Italiya da Girka dake fama da irin wannan matsala.

Wadannnan kasashen sun kasance hanyoyin shiga nahiyar ta turai ga masu gujewa tashe-tashen hankula a nahiyar Afrika da Gabas ta Tsakiya.

A watan da ya gabata ne, hukumomin kasar suka ayyana cewa za su gina wata katanga mai nisan kilomita 175 akan iyakokin Hungary da Serbia, domin dakile kwararar bakin haure.

Sama da mutane dubu-sittin hukumomin kasar suka ce sun cafke a wannan shekara kadai yayin da suke korkarin shiga kasar ta bauruniyar hanya.

XS
SM
MD
LG