Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Japan Ta Tallafawa Najeriya Da Motocin Asibiti


Najeriya ta sami tallafin motocin daukar marasa lafiya domin kai daukin gaggawa duk lokacin da bukatar hakkan ya taso.

Gwamnatin kasar Japan ta baiwa Najeriya gudunmawar motocin daukar marasa lafiya kirar Prado talatin da daya (31) kuma suna dauke da dukan kaya aikin gaggawan da ake bukata. Wannan gudunmawar rukunin farko ne na gudumawar domin rukuni na biyu na tafe.

Jakadan Japan a Najeriya, Sudanoba Kusaoke, ya kara da cewa kasar Japan, na aiki da kungiyoyi masu zaman kansu wajan raba kayan kiwon lafiya a Najeriya, cikin tallafin Japan, na inganta lamuran kiwon lafiya a Najeriya.

Motocin dai da ministan kiwon lafiya na Najeriya, Isaac Adewole, ya kaddamar bayan karbarsu a dandalin Eagle square, Abuja, ya bada umarnin turasu zuwa manyan cibiyoyin kiwon lafiya a fadin Najeriya.

Ministan yana mai baiwa Japan tabbacin aiki da motoci ta hanyar da ta dace, ya kara da cewa tallafin yazo daidai lokacin da Najeriya ke kara daukar matakan lafiya na gaggawa masamman ma ganin yadda hatsarin mota ke lakume rayukan jama’a.

Baya ga cutar Kanjamau ko Cida an tabbatar cewa babu wata hanya ta biyu mafi zama kabari kusa kamar irin hatsarin mota a Najeriya, inda a wasu lokuta akan rasa ingantattun motocin daukar marasa lafiya domin ceto rayukan wadanda suka samu hatsari da kan bukashi kulawa ta masamman.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG