Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Misra Ta Kashe 'Yan Ta'addan Arba'in


Hari a Misra

Misra ta fada a jiya Asabar cewa jami’an tsaronta sun kashe wasu ‘yan bindiga guda arba’in a wani samame da suka kai a mabuyarsu a yankunan Sinai da kuma Greater Cairo.

Samamen da jami'an tsaron suka kai ya bayan kai wani harin bam da ya auna motar bos ta ‘yan yawon bude ido a babban birnin kasar da ya kashe wasu ‘yan kasar Vietnam guda uku masu yawon bude ido da jagorarsu dan kasar Misra.

A wata sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gida dake kula da ‘yan sandan Misra ta fitar a jiya Asabar na cewa an kashe ‘yan bindigar guda goma yayin jami’an tsaro suka kai mamaya a mabuyarsu a el-Arish dake gabar teku a yakin arewacin Sinai mai fama da tashin hankali da kuma ayyukan ‘yan ta’addan Islama.

Mai’aikatar harkokin cikin gidan ta fitar da wasu hotuna da dama dake nuna gawarwakin ‘yan bindigan da aka kashe su a cikin samamen, da bindigoginsu a kusa da gawarwakin da jinni ya lullube.

Akwai yiwuwar wannan harin zai sa hukumomi su karfafa matakan tsaro a gine-ginen da masu yawon bude ido ke yawan zuwa, kamar otal-otal da gidajen ajiye kayan tarihi da wuraren shakatawa da ake kaikomo a lokacin hutun bukin sabuwar shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG