Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashe-Kashe a Jihar Filato


Mutane na kallon wajenda Bom ya fashe a birnin Jos, dake Jihar Filato.

Rikici yayi sanadiyyar kase-kashe a Jahar Filaton Najeria.

Mutane akalla hudu ne aka hallaka baya ga 6 da su ka ji raunuka a wani harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai a kauyen Gasadamari da ke Karamar Hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.

Wakiliyar Muryar Amurka a jihar ta Filato wadda ta aiko da labarin, Zainab Babaji, ta bayyana cewa an kai masu raunuka asibiti. Ta ruwaito mai baiwa Shugaban Hukumar Barakin Ladi Shawara Kan Harkokin Yada Labarai Peter Maton na cewa an kai harin ne da misalin karfe 9 na daren jiya, inda maharan su ka hallaka wani mutum guda da matarsa a kauyen Gasa, baya ga wasu matasa kuma biyu da aka kashe a kauyen Marit.

To amma Sakataren Kungiyar Miyatti Allah ta Fulani Reshen Karamar Hukumar Barikin Ladi Muhammad Adam Muhammad, ya ce batun zargin Fulani da kai harin dai shi ba shi da wata masaniya. Y ace zargi dabam tabbacin al’amari kuma dabam muddun dai ba a kama wani don kafa hujja ba. Y ace bai yadda cewa Fulani ne ba.

Zainab ta ce ko a ranar Litini ma wasu ‘yan bindiga sun hallaka Shugaban Jam’iyyar APC a yankin Kurafos na Karamar Hukumar Barikin Ladin mai suna Samuel Doro; baya ga kashe Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na shiyyar Sof da ke Karamar Hukumar Riyom mai suna Solomon Madvan.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Shiga Kai Tsaye


XS
SM
MD
LG