Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashe Tsohon Shugaban Kasa A Yemen Ka Iya Shafar Harkokin Siyasar Kasar


Tsohon Shugaban Yemen, Ali Abdullah Saleh
Tsohon Shugaban Yemen, Ali Abdullah Saleh

Wakilin Majalisar duniya duniya a Yeman zai gana da kwamitin tsaro da kuma tattaunawa akan yadda kashe tsohon shugaban kasar zai shafi harkokin siyasar kasar.

A yau Talata wakilin Majalisar dinkin duniya a Yemen, zai yi wa kwamitin tsaro bayani kwana guda a bayan da 'yan tawaye suka kashe tsohon shugaban kasar kuma abokin kawancensu, Ali Abdullah Saleh, kuma a bayan da aka samu karin tashin hankali a babban birnin kasar saboda wargajewar kawancensu.

Kakakin Majalisar dinkin duniya, Stephane Dujjaric, ya bayyanawa manema labarai cewa, yana sa ran wakilin Majalisar dinkin duniya, Ismail Ould Cheik Ahmed, zai tattauna da wakilin kwamitin tsaron kan yadda kashe Saleh zai shafi harkokin siyasar kasar.

Ya jaddada cewa a shirye majalisar take ta shiga tsakani domin kawo karshen wannan rikicin kasar Yemen, wanda tun daga 2014 ya kashe mutane har dubu 10, ya kuma jefa miliyoyin mutane cikin tsananin bukatar agajin gaggawa.

A yau talata, jami'i mai kula da ayyukan jinkai na Majalisar dinkin duniya a kasar Yemen, Jamie McGoldrick, yayi kiran da a tsagaita wuta na jinkai domin fararen hula su samu sukunin neman agaji.

Saleh ya yi mulki a Yemen har na tsawon shekaru 30, kafin a hambarar da shi a karkashin matsin lambar siyasa a shekarar 2012, amma duk da haka ya ci gaba da mulki a bayan fage inda ya hada kawance da kungiyar Houthi mai samun goyon bayan gwamnatin kasar Iran, a yayin da suka amshe iko da birnin Sanaa a shekarar 2014, suka kuma tilastawa shugaba Abdu Rabu Mansour arcewa daga kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG