Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KASUWA: Hada Hadar Kasuwanci a Kasuwar Monday Market Da Ke Birnin Ilori, Yuni 26, 2022


Yayin da ake hadahadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin Kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya kai ziyara kasuwar Monday Market da ke cikin birnin Ilori a jihar Kwara.

WASHINGTON, DC - Alhaji Auwalu Katsina, mataimakin shugaban kasuwar, ya ce an kafa kasuwar Monday Market kusan shekaru 10 zuwa 11 da suka wuce kuma kasuwar ta yi suna wajen saida kayan gwari.

Kasuwar dai ta tattaro kabilu dabam daban ciki har da Hausawa, Yarbawa, Nupawa, Fulani da sauransu, ba tare da nuna bambanci kabila ko addini ba.

Ya kuma bayyana farashin wasu kayayyakin da kuma yadda yanayi ke shafar farashinsu.

Rashin tsaro da matsalar karancin man fetur na daga cikin kalubalen da ‘yan kasuwar ke fuskanta, cewar Alhaji Auwalu.

Saurari cikakken shirin da Mustapha Nasiru Batsari ya gabatar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:48 0:00
XS
SM
MD
LG