WASHINGTON, DC - Wakilin Murya Amurka Nasiru Adamu Elhikya ya zagaya kasuwar AYA inda ya yi hira da 'yan kasuwa da suka bayyana masa farashin kayayyaki.
A wannan kasuwa dai ana saida abubuwa da yawa kama daga abinci, magunguna, kayan kwalliya da sauran kayayyakin masarufi.
A daidai lokacin da al'umar musulmi ke azumin watan Ramadan, 'yan kasuwar sun ce harkar kasuwancin yanzu ba kamar da bane.
Saurari cikakken shirin cikin sauti.