Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KEBBI: Mahukunta Na Bincike Akan Wasu Da Ake Tuhuma Da Yi Wa Wata Yarinya ‘Yar Shekara 3 Fyade


Wata karamar yarinya.
Wata karamar yarinya.

Duk da yake da yawa daga cikin gwamnatoci musamman na arewa sun yi kwaskwarima tare da saka hannu ga dokokin kare ‘yancin kananan yara, har yanzu ana samun mutanen da ke yi wa dokokin karan-tsaye suna cin zarafin yara.

Yanzu haka mahukunta a jihar Kebbi dake arewa maso yammacin kasar na gudanar da bincike akan wasu da ake tuhuma da yi wa yarinya ‘yar shekara 3 fyade.

Kasashen duniya sun yi ta fafatuka da kashe makudan kudade wajen taimakawa gwamnatoci a Najeriya a haujin inganta dokokin kare ‘yancin kananan yara, wadanda sau da yawa suke fuskantar nau'o'in cin zarafi daban daban.

Sai dai har yanzu ana samun mutanen da ke kawar da kai daga dokokin kare ‘yancin kananan yara suna cin zarafin yara musamman ‘yan mata ta hanyar yi musu fyade, kamar wanda ya faru makon jiya a garin Yauri na jihar kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya.

Jam'in gudanarwa na hukumar kare hakkin bil'adama a jihar Barrister Hamza Wala yace matasa biyu ne ake tuhuma da yi wa yarinya ‘yar shekara 3 fyade, kuma yanzu haka suna hannun hukumar tsaron ‘yan kasa ta ‘civil defence’ ana ci gaba da bincike.

Hukumar tsaron ‘yan kasa ta ‘civil defence’ ta bakin kakakinta Akeem Adeyemi tace lallai akwai magana mai kama da hakan da take bincike akai, sai dai ba zata ce komai akan batun ba, sai ta kammala bincike.

Ko bayan wannan, yanzu haka akwai wani matashi dan shekara 21 da ake zargin ya yi wa yarinya ‘yar shekara 6 fyade a garin kalgo na jihar ta kebbi wanda ‘yan sanda ke bincike akai.

Bisa ga la'akari da cewa jihar kebbi na daga cikin jihohin da suka saka hannu ga dokokin kare ‘yancin yara idan bincike ya tabbatar da laifin wadanda ake tuhuma da yin fyade, akwai yuwuwar su kare sauran shekarun rayuwar su gidan kaso, muddin dai aka yi aiki da sabuwar dokar hukumta masu aikata fyade a jihar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG