Accessibility links

Kenya ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jinkirta shari'ar da ake yiwa shugaban kasar

  • Jummai Ali

Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Kenya ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya daya jinkirta yiwa shugaban kasar da mataimakinsa shari'ar har na tsawon shekara guda, domin su samu zarafin tinkarar barazanar tsaro a Kenya.

Kasar Kenya ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya daya jinkirta yiwa shugaban kasar da mataimakinsa shari'ar har na tsawon shekara guda, domin su samu zarafin tinkarar barazanar tsaro a Kenya.

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya da mataimakinsa William Ruto suna fuskantar caje cajen aikatawa jama'a laifi a kotun kasa da kasa. Zarge zagen sun kunno kai ne daga rawar da ake zargin, sun taka a tarzomar bayan zaben shekara ta dubu biyu da bakwai data kashe fiye da mutane dubu daya da dari daya.

Jakadan Kenya a Majalisar Dinkin Duniya Macharia Kamau, yace ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi la'akari da barazanar matakan tsaro a Kenya, bayan hare haren ta'adancin watan satumba da aka kai cibiyar hada hadar kasuwancin daya kashe akalla mutane sittin da bakwai.

A wata hira da sashen Swahili yayi da Jakadan a jiya Laraba, Mr Kamau yace ya kamata shugaba Kenyatta da mataimakinsa su maida hankali wajen tinkarar barazanar tsaro a kasarsu.

Yanzu haka dai ana yiwa mataimakin shugaban Kenya William Ruta shari'a a Hague kasar Holland. Shi kuma shugaba Kenyatta an shirya a ranar sha biyu ga watan gobe na Nuwamba, idan Allah ya kaimu za'a fara yi masa shari'a.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinki Duniya bashi da ikon soke shari;ar da ake yi amma yana da ikon jinkirata yin shari'a har na tsawon watani goma sha biyu, da za'a iya sabunta duk shekara.
XS
SM
MD
LG