Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Duniya

Shugabannin Koriya Biyu Zasu Gana


Moon Jae In Da Kim Jong Un
Moon Jae In Da Kim Jong Un

An fara shirye shiryen karshe na taron koli mai dumbin tarihi tsakanin shugabannin korea ta arewa da ta kudu.

Da safe shugaban kasar korea ta Arewa Kim Jong Un zai tsallaka iyakar da sojoji sukayi wacce ta raba kasashen Koriyan biyu a kauyen Panmunjom, wuri mai tarihi inda akayi yarjejeniyar tsagaita wuta kan yakin da kasashen biyu sukeyi a shekarar 1953. Shugaban korea ta kudu Moon Jae In zai same shi a bangaren Koriya ta kudun.
Wannan zai kasance taron koli na uku tsakanin lardunan Koriya, amman zai kasance karo na farko da shugaban mulkin kwaminisanci Koriya ta Arewa zai shiga yankin Dimokaradiyya na kudu. An gudanar da Tarukan na shekarun 2000 da na 2007 a Koriya ta Arewa.
Kim zai yi tafiya da tawagar wakilai wacce ta kunshi 'yar' uwar sa Kim Yo Jong wacce ta jagoranci tawagar Koriya ta Arewa a gasar wasannin hunturu da akayi a Koriya ta Kudu, da Kim Yong Nam wanda shine shugaban kasar marar iko gudanarwa , sai kuma Kim Yong Chol wanda shine tsohon shugaban hukumar binciken asirin sojojin kasar, wanda koriya ta kudu ta dorawa alhakin nutsewar wani jirgin ruwan ta mai suna Cheonan a shekarar 2010.
Babu tabbacin matar Kim Jong Un zata kasance a cikin tawagar, a baya bayan nan ne ta bi mijin nata a wata ziyara da ya kai wa shugaban kasar Cha Xi Jingping a birnin Beijing.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG