Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kogi: Majalisa Ta Tsige Kakakinta


Jihar Kogi
Jihar Kogi

Jihar Kogi dake fama da rikicin da ya biyo byan zaben gwamna sai gashi kuma majalisar dokokin jihar ita ma ta fada cikin wani sabon rikicin da tsige kakakinta.

Bisa ga duk alamu majalisar dokokin jihar Kogi ta shiga tsaka mai wuya yayinda ta rabu biyu tsakanin masu goyon bayan kakakin da wadanda suka tsigeshi.

Yanzu dai an samu rudani a majalisar. 'Yan majalisa 17 cikin 25 suka sa hannu kan kudurin tsige kakakinta Muhammad Jimoh tare da wasu masu rike da mukamin majalisar..

Yan majalisar sun zargi kakakin da rashin iya tafiyar da sha'anin mulkin majalisar. To saidai da alama tana kasa tana dabo domin wasu masu goyon bayan kakain sun ce tsigeshi batun wargi ne. Tsigeshi sun ce ba zata sabu ba.Onarebul Umar Alfa Imam daya daga cikin masu goton bayan kakakin yace ba'a cire kakain kan ka'ida ba.

Yanzu wai shi kakakin da aka tsige ya rufe majalisar har sai watan Fabrairu na shekara mai zuwa.

Amma Onarebul Ibrahim Abdulmummuni daya daga cikin wadanda suka tsige kakakin yace kakakin ya tsigu babu wata tantama. Akan rufe majalisar zuwa hutu yace su suka ba kansu hutu ba majalisa ba. Su da aka ciresu su ne suka ba kansu hutu.

Yanzu dai su 'yan majalisa 17 sun zabi sabon kakaki wanda suka ce zai cigaba da gudanar da harkokinsu.

Masu nazari akan siyasa na ganin jihar ta kara tsunduma cikin wani yanayi na tsaka mai wuya ganin cewa tsige kakakin majalisar ya zo daidai lokacin da ake faman warware takaddama dake tsakanin sabon gwamnan jihar Yahaya Bello da mataimakinsa James Faleke.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG