Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Kudu Na Neman Sulhu Da Japan A Fannin Kasuwanci


Shugabanni Koriya ta Kuda da na Japan

Shugaban Koriya Ta Kudu, Moon Jae-in, ya ce kasarsa za ta yi farin cikin hada hannu da Japan don warware takaddar cinakayyar da ke dada tsanani tsakaninsu, muddun Japan ta yadda su hau teburin shawara.

Shugaba Moon ya yi wannan tayin ne jiya Alhamis, a yayin wani jawabi na bukin karo na 74, na zagayowar ranar kubutar da yankin ruwan Koriya din daga mulkin mallakar kasar Japan, wanda ya faru daga 1910 zuwa 1945.

Tayi mai cike da zumuncin da Shugaba Moon ya yi, na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da Koriya Ta Kudu ta bayar da sanarwar cewa, za ta sa kasar Japan cikin wani sabon rukuni game da cinakayya, wanda hakan zai takaita yawan muhimman kayakin ta ke fitarwa.

Wannan matakin, ga dukkan alamu, martani ne kan shawarar da Japan ta yanke ta cire Koriya Ta Kudu daga jerin kasashen da ta ke bai wa muhimmanci wajen kasuwanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG