Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Shirin Ganawa Da Xi A Kan Batun Hong Kong


Trump da Xi Jinping na China
Trump da Xi Jinping na China

Jiya Alhamis, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata Shugaban China Xi Jinping ya yi ganawar keke da keke da ‘yan rajin dimokaradiyya da ke zanga-zanga a Hong Kong, don kawo karshen zanga-zangar da aka kwashe makonni 10 ana yi saboda mallake yankin da China ke yi.

Shugaban na Amurka, wanda akasari tawagar motocinsa kan kauce bin inda masu yin masa zanga-zanga su ke, ya fadi ta kafar tweeter cewa idan Mr. Shi ya gana da masu zanga-zangar, wadanda akasarinsu matasa ne, a ta bakinsa, “za a kawo karshen matsalar ta Hong Hong cikin lalama da fahimta. Ba na shaka.”

Trump ya ce, “Na san Shugaba Xi sosai. Gawurtaccen Shugaba ne, wanda ke da cikakken goyon bayan mutanensa. Hakazali, ya kware sosai kan mawuyatan al’amura.

Ba na waswasi ko muskalazaratun cewa idan Shugaba Xi na son ya gaggauta warware matsalar Hong Kong cikin mutunci, zai iya. Ma’ana, ganawar keke da keke.”

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG