Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga a Hong Kong


Hong Kong
Hong Kong

‘Yan sandan Hong Kong sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan masu zanga zanga a jiya Lahadi a wasu wurare biyu na birnin da suka hada da bangaren Sham Shui Po da kuma wata babbar kasuwar gundumar Causeway Bay.

"Mu na fatan duniya ta san cewa Hong Kong ta yanzu Hong Kong din da ta sani ba ne", abin da wani daga cikin masu zanga-zangar ya gaya ma kamfanin dillancin labarai na Associated Press kenan.

Jami’an China sun bayyana rashin jin dadinsu kan kira da sakataren harkokin wajen Birtaniya Dominic Raab ya yi wa shugaban Hong Kong Carrie Lam a ranar Juma’a a game da masu zanga zanga.

China ta bukaci a cikin mutunci Birtaniya ta gaggauta daina ayyukanta na tada rikici a Hong Kong kana ta daina tsoma baki a harkokin China, inji mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG