Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ba Da Belin Maryam Sanda Da Ake Tuhuma Kan Kashe Mijinta


Maryam Sanda a wani lokaci da ta ke fita daga kotu dauke da 'yarta
Maryam Sanda a wani lokaci da ta ke fita daga kotu dauke da 'yarta

An ba da belin Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta a watan Nuwambar bara, bayan da suka samu sabani a gidansu da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Wata kotun tarayya da ke zama a Abuja ta ba da belin Maryam Sanda, matar da ake tuhuma da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello, a cewar jaridun Najeriya.

Alkali Yusuf Halilu ne ya ba da belin Maryam bisa dalilai na rashin lafiya.

A bayan kotun ta sha watsi da bukatar a ba da belinta har sau uku a cewar jaridar Daily Trust.

Lauyan ‘yan sanda da ke tuhumarta, CSP James Idachaba, ya kalubalanci wannan matsaya da kotu ta dauka.

Amma kotun wacce ke zama a unguwar Jabi, ta yanke shawarar cewa dalilan rashin lafiya da lauyanta, Cif Joseph Daudu (SAN) ya gabatar, sun gamsar da ita.

A baya Daudu, ya gabatar wa da kotun cewa Maryam na dauke da juna biyu a zaman da aka yi a ranar 6 ga watan Fabrairu.

Mai shari’ar Halilu ya ba da belin ne da sharadin cewa sai Maryam ta gabatar da mutane biyu da suka mallaki kadarori a Abuja.

Sannan kotun ta bukaci mahaifin Maryam ya saka hanu akan ya amince cewa zai rika gabatar da ita a gaban kotun a duk lokacin da aka bukaci ganinta.

Maryma Sanda, ‘ya ce ga tsohuwar shugabar bankin Aso Savings, Maimuna Aliyu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG