A cikin watan Nuwamban bara ne ya amsa laifin ya aikewa masallacin da ake kira Tawfiq Islamic Center wasikar da a ciki, yayi barazanar "zai tarwatsa masallacin tare da duk 'yan ketare dake cikinsa."
Fisher dan shekaru 57 da haifuwa, yace ya juma yana jin haushin musulmi tun lokacinda 'yan ta'adda suka kawo harin ta'addanci anan Amurka a shekara ta 2001, tun can yake son hana musulmi gina masallaci a unguwarsu.
"Wannan hukuncin ya aike da sako ga duk wanda yayi barazanar tada tarzoma kan wadansu mutane saboda kiyayyar addini, zai fuskanci hukunci mai tsanani," inji mukaddashin mataimakin Atoni Janar Tom Wheeler, ya fada jiya Laraba.
Facebook Forum